Hukumar Kula da Sufurin Ababen Hawa ta Jihar Kwara( KWARTMA) ta ce mutane 18 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da wata babbar motar shanu da kuma wata ƙaramar mota ƴar ƙurƙura akan babban titin Oko-Olowo dake Ilorin.
Olawuyi Gani mai magana da yawun hukumar ta KWARTMA shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya aikawa da manema labarai a ranar Alhamis.
Gani ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Laraba lokacin da motar tirelan dake ɗauke da shanu da kuma mutane ta ci karo da wata mota ƴar ƙurƙura tana tsaka da shara gudu abun da ya kawo mummunan karo da ya lakume rayuka.
Ya ƙara da cewa hatsarin da ya haɗa da motar shanun mai rijistar namba TRL014GZ ya faru ne da misalin karfe ƙarfe 03:34 na rana kuma jami’an hukumar da na hukumar FRSC sun yi gaggawar kai ɗauki zuwa wurin.