An kama wasu ƴan Najeriya da suka aikata fashi a ƙasar Kuwait

Hukumomin tsaro a ƙasar Kuwait sun kama wasu ƴan Najeriya biyu da ake zargi da aikata fashi da makami a wani wurin musayar kuɗaɗe.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyu sun yi awon gaba da kuɗin da yawansu yakai dalar Amurka $14,918 a lokacin fashin.

Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta tabbatar da kama mutanen inda ta ce tuni aka miƙa mutanen da ake zargi da kuma abin da suka sata ga ofishin babban mai gabatar da ƙara na ƙasar.

Jaridar Arab Times ta ce jami’an sashen binciken manyan laifuka a gundumar mulki ta Ahmadi su ne suka samu nasarar kama mutanen ƙasa da sa’o’i 24 bayan aikata laifin.

Bincike ya nuna cewa mutanen sun ɗauki tsawon lokaci cikin nutsuwa suna tsara yadda za su yi fashin  ta hanyar sanya idanu daga saman wani bene kan wurin musayar kuɗaɗen.

More from this stream

Recomended