Mayaƙan sun ISWAP sun kashe sojoji 5 a Borno

Mayaƙan ƙungiyar ƴan ta’adda ta ISWAP sun kashe dakarun sojan Najeriya biyar a wani harin kwanton ɓauna da suka kai musu a jihar Borno.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi ya rawaito cewa harin ya faru a ranar 4 ga watan Janairu a Sabon Birni dake ƙaramar hukumar Damboa ta jihar.

Rahoton ya bayyana cewa harin kwanton ɓaunar ya haifar da musayar wuta ta tsawon sa’o’i biyu abin da ya kai ga lalata kayan yaki da dama.

Ana ta bangaren rundunar sojan saman Najeriya a matsayin martani kan harin ta yi luguden wuta kan matartarar ƴan ta’addar na ISWAP dake Timbuktu a dajin Sambisa.

More from this stream

Recomended