Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci tawagar gwamnatin jiharsa zuwa Jihar Bauchi domin mika ta’aziyya ga Gwamna Bala Mohammed, wanda ya rasa abokiyar zaman mahaifiyarsa kwanan nan.
A jawabinsa, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai kyawawan halaye da jajircewa, wacce ta bayar da muhimmiyar gudunmawa ga iyalanta da al’ummarta.
Ya ce: “Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta mata, ya sanyata a cikin Aljanna Firdausi, kuma ya bai wa iyalanta ƙarfin hali don jure wannan babban rashi.”
Ziyarar ta’aziyyar ta nuna zumunci da goyon baya tsakanin jihohin Kano da Bauchi a irin wannan lokaci mai cike da alhini.