Hukumar Kwastam ta Najeriya ta yi wa jami’anta 1,419 ƙarin matsayi

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta amince da karin girma ga ma’aikata 1,419 masu matsayi na ƙananan jami’ai a hukumar.

Haka zalika, Hukumar Kwastam ta shiyya ta Ogun 1 ta gudanar da taron tsare-tsare tare da shugabannin ƙungiyar Ƙwararrun Editoci da Masu Ilimin Jama’a (NASRE) a ofishinta, inda suka tattauna muhimmancin haɗin gwiwa wajen tabbatar da tsaron ƙasa da sauƙaƙa kasuwanci.

Kakakin hulɗa da jama’a na ƙasa, Abdullahi Maiwada, ya bayyana cewa jerin sunayen waɗanda aka ba karin girman sun haɗa da jami’an General Duty da Support Staff waɗanda suka yi fice a jarabawar karin girma ta shekarar 2024.

A cewarsa, an ɗaga jami’ai 346 daga General Duty da 384 daga Support Staff daga matsayin Assistant Inspector of Customs (AIC) zuwa Inspector of Customs (IC). Haka kuma, jami’ai 4 daga General Duty da 13 daga Support Staff sun sami karin girma daga matsayin Customs Assistant I (CAI) zuwa Assistant Inspector of Customs (AIC).

More from this stream

Recomended