Yadda wani mutumi ya banka wa kansa wuta bayan matarsa ta ƙi sasantawa da shi

Wani mutum wanda ba a bayyana sunansa ba ya mutu bayan ya banka wa kansa da matarsa wuta a unguwar Ijoka da ke Akure, Jihar Ondo.

Rahotanni sun nuna cewa ma’auratan, waɗanda suka yi aure na tsawon shekaru goma kuma suka haifi yara biyu, sun rabu sakamakon wata matsala ta aure da ba a bayyana ba.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana faruwar lamarin a shafinta na X a ranar Juma’a.

‘Yan sanda sun ce wanda ya rasu ya aikata wannan mummunan abu ga kansa da matarsa bayan ya roƙe ta da su sasanta, amma ta ƙi amincewa da kawo ƙarshen rikicin.

Wata majiya daga ‘yan sanda, wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin magana kan lamarin, ta ce: “Mutumin ya rabu da matarsa tsawon wani lokaci, amma ya sha roƙonta ta kawo ƙarshen matsalar auren su kuma su ci gaba da zama tare a matsayin ma’aurata. Duk da haka, matar ta ƙi amincewa.”

More from this stream

Recomended