Tashin bam ya yi ajalin manomi a jihar Neja

Wata fashewar bam a ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja ta yi sanadin mutuwar wani manomi mai suna Isyaku Gambo.

Rahotanni sun bayyana cewa, marigayin ya taka kan bama-baman ne yayin da yake kan babur ɗinsa, yana jigilar amfanin gona daga gona zuwa gida.

Ana zargin cewa an binne bama-baman ne a kan hanya tsakanin ƙauyen Unguwan-Usman da Bassa, wanda fashewarsa ta ragargaza jikin mamacin.

Wani majiya ya shaida wa Daily Trust cewa, “Lamarin ya faru ne a yau (Asabar), misalin ƙarfe 3 na rana, lokacin da mamacin yake dawowa daga gona inda ya je ɗebo kayan gona. Wannan shi ne karo na farko da muka fuskanci irin wannan abu, kuma ana zargin ‘yan ta’adda ne suka binne bama-baman.”

Duk da yunƙurin da aka yi don jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ba a samu nasara ba.

More from this stream

Recomended