Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Daurin Rai da Rai Kan Fyade

A ranar Alhamis, Mai Shari’a Modupe Osho-Adebiyi na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Laminu Ahmed mai shekara 36 hukuncin daurin rai da rai, kan laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara bakwai fyade.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya jagoranci samun nasarar wannan hukunci.

A yayin da take yanke hukunci, Mai Shari’a ta bayyana cewa lauyan mai gabatar da ƙara daga sashen hana cin zarafi da kuma fyade (Sexual and Gender-Based Violence Unit) na Ma’aikatar Shari’a, karkashin jagorancin Mrs. Yewande Awopetu, sun yi nasarar tabbatar da laifin.

A ranar 3 ga watan Janairu, 2023, wanda aka yanke wa hukunci ya nemi yarinyar (wadda ba a bayyana sunanta ba) ta kawo masa abinci daga cikin abincin da mahaifiyarta ke siyarwa a kasuwar kayan lambu ta Zuba, Abuja. Daga nan sai ya yaudare ta ta biyo shi zuwa wani ɗakin bayan jama’a a kasuwar.

Da ta shiga ɗakin bayan, sai ya rufe ƙofar sannan ya fara cin zarafinta ta hanyar tilasta mata ta hanyar sumbatar ta, sanya yatsansa cikin farjinta, sannan ya yi mata fyade.

Ya kuma rufe mata baki a lokacin da ta yi ƙoƙarin yin ihu, tare da yi mata barazanar kashe ta idan har ta bayyana abin da ya faru ga kowa.

Sai dai, yarinyar ta bayyana wa mahaifiyarta abin da ya faru da ita a lokacin da ta koma gida. Mahaifiyar yarinyar ta bar gida zuwa taron suna a lokacin da wannan abin ya faru.

More from this stream

Recomended