Lakurawa sun fara tserewa daga jihohin Kebbi da Sokoto

Rahotannin dake fitowa daga jihohin Kebbi da Sokoto na nuna cewa ƴan ƙungiyar ƴan ta’addar Lakurawa na janyewa daga wuraren da suke a sakamakon luguden wuta da sojoji suke musu.

Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi ya bayyana cewa haɗin gwiwar dakarun sojan sama da na ƙasa sun kai farmaki kan sansanonin Lakurawa dake jihohin biyu tare da gano wasu shanu  da ƴan ta’adda suke sayarwa domin samun kuɗaɗen amfani.

Rahoton ya bayyana cewa harin na haɗin gwiwa ne tsakanin dakarun rundunar Operation Fansar Yamma da kuma Operation Farautar Mujiya.

Makama ya ce ƴan ta’addar na janyewa ya zuwa yankin Borgu dake kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin sakamakon farmakin.

Wasu bayanan sirri na nuni cewa ƴan ta’addar za su iya nausawa kudu zuwa Ilesha Ibaruba dake jihar Kwara a kusa da jamhuriyar ta Benin inda haramtattun aikinsu ba zai fuskanci sanya ido sosai ba.

More from this stream

Recomended