Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International tayi allawadai da yadda aka gurfanar da wasu ƙananan yara a gaban kotu da ake zarginsu da shiga cikin zanga-zangar tsadar rayuwa ta #Endbadgovernance.
A cikin wasu jerin sakonni da kungiyar ta Amnesty ta wallafa a shafinta na X da aka fi sani da Twitter a baya ta ce kama yaran da aka yi bai dace ba ya saɓawa doka ta ce yin haka ya nuna yadda gwamnati ta ke watsi da bin doka.
Amnesty ta ce ya kamata gwamnati ta bayar da umarnin sakin dukkanin yaran ba tare da gindaya wasu sharuɗa ba.
Yunkurin yiwa yaran shari’a kan zargin cin amanar kasa ba dai-dai ba ne kuma kokari ne na daƙile ƴancin faɗar albarkacin baki.
Kungiyar ta ce dole shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka a saki yaran da aka kama tun watan Agusta ba tare da an gindaya wasu sharuɗa ba.
A yau ne aka gurfanar da yaran a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja inda ake zarginsu da laifin cin amanar ƙasa.
Halin yunwa da yaran suke ciki ya tayarwa da miliyoyin mutane hankali.