Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya dakatar da Auwal Danladi Sankara kwamishinan ayyuka na musamman na jihar kan zargin da ake masa na lalata da matar aure.
A ranar Juma’a ne hukumar Hisba ta jihar Kano ta sanar da kama Sankara a cikin wani gida da ba a kammala ba tare da wata matar aure inda hukumar ta zarge shi da aikata baɗala.
A wata sanarwa ranar Asabar, sakataren gwamnatin jihar, Bala Ibrahim ya ce an dakatar da kwamishinan har sai an kammala binciken laifin da ake zarginsa da aikatawa.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne a matsayin kariya domin gudanar da cikakken bincike.
“Mun ɗauki dukkanin zarge-zarge da muhimmanci kuma mun bada muhimmanci wajen tabbatar da yardar da mutanen Jigawa suka yi wa gwamnati,” ya ce.
Sai dai kwamishinan ya musalta zargin da ake masa kuma ya ci alwashin gurfanar da hukumar ta Hisba a gaban kotu.