Tinubu zai wuce Paris daga London

Shugaba Bola Tinubu na shirin zuwa birnin Paris na kasar Faransa daga birnin Landan na kasar Birtaniya, a kowane lokaci daga yanzu don wani ‘muhimmiyar hulda’.

Wani makusancin siyasa na Tinubu, Ibrahim Kabir Masari ne ya bayyana hakan a yammacin ranar Juma’a.

Rahotanni sun ruwaito cewa, Shugaba Tinubu ya tafi Landan ne a ranar 2 ga Oktoba, 2024, domin hutun makonni biyu.

Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce “hutun aiki” wani bangare ne na hutunsa na shekara. 

An kuma ce shugaban zai dawo Najeriya bayan kammala hutun.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja yau zuwa kasar Ingila domin fara hutun makonni biyu, na hutun shekara.

Sanarwar ta ce “zai dawo kasar bayan hutun ya kare.”

More from this stream

Recomended