Kotu ta yanke wa matashin da ya yi lalata da ƙaramar yarinya hukuncin ɗaurin shekara 8

Mai shari’a Rahman Oshodi na kotun laifuffukan lalata da cin zarafin cikin gida a jihar Legas da ke Ikeja ya yanke wa wani matashi mai suna David Charles hukuncin daurin shekaru takwas a gidan yari bisa samunsa da laifin cin zarafin wata karamar yarinya ‘yar shekara 10 da haihuwa.

Mai shari’a Oshodi ya yanke hukuncin ne bayan Charles ya amsa laifin tuhume-tuhume biyu da gwamnatin jihar Legas ta gabatar masa a ranar 28 ga Yuli, 2021.

Jihar ta shaida wa alkalin yayin shari’ar cewa wanda ake tuhuma a ranar 16 ga Afrilu, 2017, ya taba cinyar yarinyar ‘yar shekara 10 da azzakarinsa inda yakw nuna mata hotunan batsa a lamba 16 Aina Street, Shogunle, Oshodi, Legas.

Mai gabatar da kara ya dage cewa laifukan sun sabawa Sashe na 135 da 170 kuma ana hukunta a kansu ne a karkashin Sashe na 172 na dokar laifuka, Ch, C.17, Vol.  3, Dokokin Jihar Legas, 2015.

A lokacin da ake shari’ar, mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu, kuma wanda ake tuhumar ya bayar da shaida a madadinsa kafin daga bisani ya zabi yin sulhu.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Oshodi ya bayyana cewa, kotun ta yi nazari sosai kan gaskiyar lamarin, da yarjejeniyar sulhu da kuma tanade-tanaden doka.

More from this stream

Recomended