Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam’iyar NNPP ya zuwa jam’iyar APC.

Ali Jita ya sanar da sauya sheƙar tasa a yayin wata ziyarar ban girma da yakai a gidan Barau dake Abuja kamar  yadda mai taimakawa mataimakin shugaban majalisar dattawan kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Mudashir ya sanar.

Barau ya yabawa Ali Jita kan sauya shekar da yayi ya zuwa APC.

Ana sa jawabin Ali Jita ya bayyana yadda yake sha’awar siyasar Sanata Barau inda ya ce dama soyayyarsa da Kwankwaso ce tasa ya shiga jam’iyar NNPP kuma a yanzu ya fita ya koma APC.

A ƴan kwanakin nan ana ta samun mutane da suke ficewa daga jam’iyar NNPP suna komawa APC tsarin tafiyar gidan Sanata Barau.

More from this stream

Recomended