Sanata Ifeanyi Ubah ya mutu a Londan

Ifeanyi Ubah sanata mai wakiltar mazaɓar kudancin jihar Anambra a majalisar dattawa ya mutu.

Rahotanni sun bayyana cewa sanatan ya mutu ne ranar Juma’a da daddare a birnin London bayan da ya yanke jiki ya faɗi a wani otal.

Yemi Adaramodu shugaban kwamitin hulɗa da jama’a na majalisar dattawa ya tabbatar da mutuwar sanatan  a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya bayyana a marigayin wanda ya bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban ƙasarnan.

More from this stream

Recomended