Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna sun kama wasu mutane 143 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ‘yan fashi da makami a sassa daban-daban na jihar a tsakanin watan Mayu zuwa Yunin 2024.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Audu Dabigi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan da ke Kaduna a ranar Alhamis, inda aka baje kolin makaman da ‘yan sandan suka kwato.
Ya ce wadanda ake zargin sun hada da ‘yan fashi da makami 73 da ‘yan bindiga 70 da suka hada da ‘yan fashi da makami da ake nema ruwa a jallo, Bello wanda aka kama a lokacin da yake shirya laya ga wasu ‘yan fashin domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Ya kara da cewa a kalla ‘yan bindiga tara ne jami’an rundunar suka kashe a cikin watanni biyu da suka gabata.