APC ta faɗi zaɓe a Kano Saboda Rikicin Ganduje da  Sanusi a cewar Lukman

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyar APC na ƙasa a shiyar arewa maso yamma, Salihu Lukman ya ce jam’iyar APC ta faɗi zaɓen 2023 a jihar Kano ne saboda, Abdullahi Umar Ganduje tsohon gwamnan jihar.

A wata sanarwa ranar Litinin, Lukman ya ce rikicin Ganduje da Muhammadu Sanusi II bai yi dace ba.

Jigon a APC na magana ne biyo bayan turka-turkar da ta biyo sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Ganduje wanda shi ne shugaban jam’iyar APC na ƙasa ya sauke Sanusi daga mulkin a shekarar 2020 kana ya rarraba masarautar Kano ya hanyar ƙirƙirar ƙarin wasu masarautun.

More from this stream

Recomended