Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da belin tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da kuma wasu mutane uku kan kuɗi naira miliyan 100 kowannen su.
Hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ce ita gurfanar da Sirika tare da ƴarsa Fatima a gaban Mai Shari’a Sylvanus Oriji na babbar kotun birnin tarayya Abuja dake Maitama a ranar Alhamis.
Ƙarin waɗanda aka gurfanar sun haɗa da Jalal Hamma tare da wani kamfani Al-Duraq Investment Ltd inda ake tuhumarsu da wawashe dukiyar al’umma har naira biliyan biyu da miliyan ɗari bakwai.
A cewar takardun ƙarar Sirika ya yi amfani da matsayinsa na ministan Sufurin Jiragen Sama inda ya riƙa bawa kansa kwangila, sirikinsa da kuma makunsantarsa.
A yayin da kotun ke sanar da hukuncin kotun ta ce dole kuma su kawo mutane biyu da za su tsaya musu.