Kotu Ta Hana PDP Cire Shugaban Riƙon Jam’iyar

Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta hana jam’iyar PDP dakatar da Umar Damagum daga matsayinsa na shugaban riƙon jam’iyar.

Mai Shari’a  Peter Lifu shi ne ya bayar da umarnin gaggawar a ranar 3 ga watan Mayu da ya hana jam’iyar zaɓar wani mutum domin ya maye gurbin Damagum har sai an kammala shari’ar da aka shiga gabansa.

Umar El-Gash Maina and Zanna Mustapha Gaddama sune suka shigar da ƙarar mai namba FCH/ABJ/CS/579/2024 a gaban kotun ranar 2 ga watan Mayu.

Waɗanda ake ƙara a shari’ar sun haɗa da kwamitin zartarwar jam’iyar, kwamitin amitattun jam’iyar, shugabannin jam’iyar da kuma hukumar zaɓe ta INEC.

Kotun ta dage sauraron ƙarar ya zuwa ranar 14 ga watan Mayu.

More from this stream

Recomended