Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin a ɗaura musu aure.
Gwamnan ya rattaba hannu ne akan dokar a wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar a gidan gwamnati jihar da ya samu halartar shugaban majalisar dokokin jihar.
A cewar mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa daga yanzu babu wani aure da za a ɗaura a jihar ba tare da an gabatar da takardar shedar yin gwaje-gwajen ba
Gwaje-gwajen sun haɗa da na ciwon hanta, cutar HIV, ƙwayoyin halitta da kuma sauran cututtukan da za iya ɗauka ta hanyar jima’i.
Ya ce dokar ta zama dole domin kawo ƙarshen yaran da ake haifa da cutar sikila, HIV da kuma cutar hanta.