Gwamnan Edo Zai Fara Biyan 70,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan ga ma’aikatan jihar inda za a riƙa biyan naira dubu 70,000.

Gwamnan ya sanar da haka a ranar Litinin a wurin bikin buɗe ginin sabon ginin da ake Kira Gidan Ƴan Kwadago.

Obaseki ya ce gidan na ƴan ƙwadago za a riƙa kiransa da sunan tsohon gwamnan jihar, Kwamared Adam Oshiomhole.

Sabon mafi ƙarancin albashin zai fara ne daga ranar 1 ga watan Mayun 2024 a a cewar gwamnan .

Kungiyoyin kwadago na TUC da NLC sun jima suna fafutukar ganin an yi ƙarin albashi ga ma’aikata duba da yadda aka samu hauhuwar farashin kayayyaki da kuma cire tallafin man fetur da aka yi.

More from this stream

Recomended