An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan bauna da aka kai musu.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis kuma an ajiye gawar marigayin, Manjo a rundunar soji a wani asibiti a Katsina.

An tattaro daga majiya mai tushe cewa an kai harin ne a kauyen Malali da ke cikin karamar hukumar Kankara.

Daga nan ne aka kira shi da ya bayar da hadin kai domin dakile harin da aka kai kauyen.

Bayan haka kuma sai rai ya yi halinsa.

More from this stream

Recomended