Mambobin jam’iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje.
Majalisar zartarwar yankin Ganduje karkashin jagorancin Haruna Gwanjo ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano ranar Litinin.
Gwanjo ya ce dole ne tsohon gwamnan ya wanke sunansa daga zargin cin hanci da rashawa dangane da shari’ar dala da ta dade ana yi.