An shiga zaman zullumi bayan da aka zargi jami’an hukumar tsaro NSCDC wato Civil Defence da harbe wata mata a filin sallar Idi dake Gusau a jihar Zamfara.
Jami’an na Civil Defence sun buɗe wuta ne lokacin da suka biyo wasu ɓata gari a wajen sallar Idin inda harsashi ya yi kuskuren samun matar.
Daga bisani wasu matasa da suka fusata sun ƙona wata mota ƙirar Hilux ta da jami’an tsaron suka zo da ita tare da jikkata wasu daga ciki.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar ya ce jami’an suna tsare da jami’an NSCDC guda biyu a hannunsu inda ya ƙara da cewa ana cigaba da bincike kan lamarin.