Darajar Naira Ta Ƙara Yin Sama A Kasuwar  Musayar Kuɗaɗe

Darajar takardar Kuɗin naira tayi sama a kasuwar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje ta bayan fage inda aka riƙa canza dalar Amurka akan ₦1250.

Hakan na nuna cewa darajar takardar kuɗin na naira tayi sama da kaso 0.43 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda akayi musayar ta kan ₦1280 a ranar 29 ga watan Maris.

Masu musayar kuɗaɗe  a Lagos wanda aka fi sani da bureau de change a turance sun ce suna sayan  kowace dala akan  ₦1230 kuma su sayar akan ₦1250 wato ribar ₦20 ne kenan.

A kasuwar musayar kuɗaɗe ta bankuna darajar naira tayi ƙasa inda ake musayar dalar Amurka akan ₦1309.39 a ranar 28 ga watan Maris a maimakon ₦1300.43 a ranar 27 ga watan Maris.

More from this stream

Recomended