Ƴansanda sun yi nasarar kama sojan bogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce ta kama wani sojan bogi da ake zargi da aikata laifukan yaki, wanda sojoji suka bayyana suna nema ruwa a jallo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar da misalin karfe 3:00 na rana a unguwar Ijegun da ke Legas.

Mista Hundeyin ya ce an kama wanda ake zargin ne a yayin wani sintiri na yau da kullun da rundunar ‘yan sanda ta Ijegun ta yi a unguwar Fagbile Estate, Ijegun, a Sherin Oshun.

Ya ce rundunar ‘yan sintiri ta kama mutumin mai suna Sajan Manjo (wannan wani suna ne da aka sakaye), cikin kakin soja, wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen yin katsalandan.”

“Nan da nan muka aika a kirawo kwamandan tsaron sojan da ke jagorantar bututun mai a Ijeododo, domin ya zo ya tantance wanda ake zargi.

“Sojoji sun tabbatar da cewa sojan bogi ne.  A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin.

“Sojoji sun tabbatar da cewa yana cikin jerin sunayen da ake nema ruwa a jallo. Za a gurfanar da shi a kotu idan an kammala bincike,” inji shi.

More from this stream

Recomended