Gwamnatin Kano Ta Karɓi Motocin Kayan Abinci 195 Daga Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da karɓar jumullar motoci 195 maƙare da nau’ikan hatsi domin rabawa mutane dake faɗin ƙananan hukumomin jihar 44.

Gudunmawar wani ɓangare ne na tallafi da  gwamnatin tarayya ta bayar domin ragewa mutane raɗaɗi musamman a lokacin da Musulmi suke gudanar da azumin watan Ramadan.

A wurin wani taron manema labarai a ranar Lahadi, Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya ce, “Jihar ta kuma karɓi jumullar motoci 100 na ƙaramin buhun  shinkafa 25Kg, motoci 44 na Dawa,motoci 14 na Gero da motoci 41 na Masara da za a raba a mazaɓun  484 dake ƙananan hukumomin jihar 44 a cikin makon da muke ciki.”

Bature ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na cigaba da ƙoƙarin sayo ƙarin motoci 132 na ƙaramin buhun shinkafa 25Kg da za a raba a faɗin jihar.

More from this stream

Recomended