Ƴan fashin daji sun sace almajirai 15 daga wata makarantar Allo dake ƙauyen Gidan Bakuso a ƙaramar hukumar Gada ta jihar Sokoto.
Rahotannin da suka fito daga ƙauyen sun bayyana cewa an sace ɗaliban ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Asabar.
An jiyo, Mallam Liman Abubakar da ya mallaki makarantar na cewa yara 15 ne kawo yanzu ba a gani biyo bayan kai harin.
Abubakar ya ce ƴan fashin dajin sun farma ƙauyen ne inda suka harbi mutum ɗaya tare da sace wata mata ɗaya kafin su kai farmaki kan makarantar allon .
“A lokacin da suke fita daga garin sai suka hango ɗaliban mu suna guduwa ya zuwa daƙunan kwanansu sai suka yi garkuwa da yawa daga cikinsu” Abubakar ya ce.
“Mun ƙirga mutane 15 da ba a gansu ba kawo yanzu kuma muna cigaban da neman waɗansu.”
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Sokoto Ahmad Rufa’i bai tabbatar da faruwar lamarin ba amma ya ce an tura jami’an tsaro ya zuwa yankin domin su gano abun da ya faru.