Matashin mai tuƙa keke-napep ɗin nan, mai shekaru 23 a Kano, Awwalu Salisu, wanda ya mayar da makudan kudi Naira miliyan 15 da wani dan kasar Chadi ya bari a babur dinsa a shekarar 2023, an ba shi tallafin karatu har zuwa matakin digiri na uku, wadda darajarsa ta kai naira miliyan 250.
Labaran Shugabanci
Jaridar Leadership ce ta yi bikin karrama Awwalu a ranar Talatar da ta gabata a wajen taron shekara-shekara da kuma bikin bayar da lambar yabo a matsayin wanda ya lashe lambar yabo ta ‘Fitaccen matashin shekara ta 2023’ saboda gaskiya da ya yi.
An karrama Awwalu, matashi ɗan Kano da ya tsinci miliyan 15 ya mayar ga mai su
