Rundunar yan ƴansandan jihar Kano ta samu nasarar kama wani matashi da suka yi garkuwa da wani yaro mai shekaru 14 a garin Mariri dake ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.
Matashin da aka kama mai suna Isma’il Adam ɗan shekara 22 sun haɗa baki da wani abokinsa da ake kira Isi wanda yanzu haka ya cika wandonsa da iska wajen aikata laifin.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano, ASP Abdullahi Kiyawa ya ce wani mutum ne ya kawo korafin cewa an sace masa ɗansa ranar 07/02/24.
Kiyawa ya ce biyo bayan samun korafin ne rundunar ta shiga aiki ba dare ba rana har ta kai ga an kama wanda ake zargin.
Matashin ya bukaci a biya su kuɗin fansa naira miliyan 4 ta hanyar yin amfani da wayar abokinsa ba tare da saninsa ba.
Tun da farko abokin wanda aka yi amfani da wayarsa wajen cinikin kuɗin fansar ya ce Isma’il ne ya ari wayarsa ne da zummar zai dawo masa da ita washegari amma kuma ya shafe kwanaki ba tare da ya dawo da ita ba.
Da yake amsa tambayoyi Adamu ya ce sun sace Abdullahi ne kana sun yanka shi a cikin wani kango tun gabanin su nemi a biya su kuɗin fansa.