Sojojin Ruwa Sun Kama Mutane 11 Dake Ƙoƙarin Gina Haramtacciyar Matatar Man Fetur A Jihar Rivers

Rundunar Sojan Ruwan Najeriya ta ce ta kama wasu mutane 11 da ake zarginsu da yinkurin gina Haramtacciyar matatar man fetur a jihar Rivers.

Saidu Kabir jami’in dake kula da jirgin ruwan rundunar da ake kira NNS Pathfinder dake Fatakwal ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a yayin da ake gudanar da aikin sintirin yaƙi da satar ɗanyen mai a mashigar ruwa ta Krakrama dake jihar Rivers.

Kabir ya ce an miƙa mutanen da ake zargi a hannun Monday Lawal kwamandan rundunar NSCDC dake jihar Rivers.

An kama mutanen ne a ranar 23 ga watan Janairu a cikin wani jirgin wanda ke ɗauke da kayayyakin gina matatar.

More from this stream

Recomended