Ƴan sanda sun kama mai garkuwa da mutane a Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba ta ce ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne.

Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da babban birnin tarayya Abuja Haruna Garba ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a kauyen Sauka a ranar 21 ga watan Janairu, kuma an ceto wanda aka yi garkuwa da shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa, jami’an ‘yan sanda daga sashen Iddo, sun samu kiran waya cewa wasu ‘yan bindiga cikin wata bakar Toyota Corolla sun harba tayoyin wata mota kirar Prado Jeep ta wani Suleiman Sabo.

Malam Garba ya ce Malam Sabo, wanda zai je gidansa da ke Sabon Lugbe, an tilasta masa tsayawa ne sai suka cusa shi cikin motarsu, inda ya bar Prado Jeep dinsa da matarsa.

More from this stream

Recomended