Gwamanti Tarayya ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewa za a mayar da Legas babban birnin Najeriya

Fadar shugaban kasa ta musanta rade-radin da ake yi kan yunkuri na mayar da birnin tarayya zuwa Legas, inda ta jaddada cewa irin wannan ikirarin ba shi da tushe balle makama da siyasa.

Bayo Onanuga, mai ba da shawara na musamman kan yada labarai da dabarun shugaba Bola Tinubu, ya yi watsi da jita-jitan, ya kuma zargi masu yada su da rashin gaskiya da kabilanci.

Onanuga ya fayyace cewa mayar da hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN) zuwa Legas kwanan nan ba ya nufin wani yunkuri na mayar da babban birnin tarayya can, domin gyaran da FAAN ta yi wani mataki ne kawai na gudanarwa na daidaita inda take da cibiyar masana’antar sufurin jiragen sama a Legas.

Ya jaddada cewa matsayin Abuja a matsayin babban birnin kasar an kafa shi bisa doka kuma ba zai canza ba.

More from this stream

Recomended