Ƴan sanda sun kama wani kasurgumin dan daba a Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani da ake zargin ya cire hannun wani matashi dan shekara 25 tare da daba masa wuka a kai.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce wanda ake zargin ya kasance cikin jerin sunayen ‘yan sanda na tsawon shekaru biyu da ake nema ruwa a jallo bisa laifin dabanci da kuma haddasa mummunar barna.

Ya ce wanda ake zargin ya aikata laifin tare da wasu mutane biyu.

Ya kara da cewa, dubunsa ta cika ne a lokacin da ‘yan sandan da ke sintiri suka kai samame a wata maɓoya a wata unguwa da ke wajen birnin Bauchi suka kama shi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ranar Asabar 22 ga Yuli, 2023 da misalin karfe 6:30 na yamma, jami’an ‘yan sanda da ke hedikwatar ‘C’ Divisional hedkwatar ‘C’, a lokacin da suke aikin sintiri, suka gano tare da kai samame a wata maɓoya da ke Sabon Layi da ke wajen birnin Bauchi, wanda ya kai ga kama wani mutum mai suna Muhammad Abdullahi, wanda aka fi sani da Luwawu.”

Related Articles