Direba ya ciji kunnen wani jami’in VIO

An sami rashin jituwa a Warri a yayin da wani direban Sienna ya cije kunnen Papu Prosper, jami’in binciken ababen hawa (VIO), a lokacin da suke yin sintiri a garin Warri na jihar Delta.

Gabaɗayan gardamar ta kasance akan takardun abubuwan hawa ne da suka yi isfaya a safiyar Juma’a.

“Ni jami’in binciken ababan hawa ne, VIO, mun je sintiri a garin Warri, inda muka rike wani direba, wanda takardunsa sun yi isfaya, shugabana ne ya sa ni in bi shi ofishinmu da ke Warri don duba ko takardunsa sun yi isfaya,” a cewar Prosper.

Ya ƙara da cewa, “A lokacin da nake bin mutumin, sai ya ce zai kashe ni, sai ya fito da wata wuka ya soka min, sai na yi ta faman fita daga cikin motar da gudu take gudu, ina fada da shi don tsira da raina a lokacin da ya cije. daga kunnena ya fadi kasa.”

Daga bisani, direban Siennar ya yi tsalle daga motar ya gudu bayan faruwar lamarin, ya bar motarsa a wajen.

More from this stream

Recomended