Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma ta tsare wasu jami’an makarantu 20 da ke da alaka da jarabawar kammala manyan makarantu a yammacin Afirka
Kamen dai an yi shi ne a fadin kasar.
Patrick Areghan, shugaban ofishin majalisar na kasa ne ya bayyana haka a lokacin da yake gudanar da aikin sa ido a wasu makarantu a ranar Alhamis a Legas.
Ya kuma kara da cewa hukumar ta WAEC ta mika duk wadanda suka aikata laifin ga ‘yan sanda domin hukunta su.
Areghan ya yi alkawarin cewa majalisar za ta dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an bi da su yadda ya kamata.