An hallaka ƴan ta’adda a Borno

Sojoji sun hallaka aƙalla ‘yan ta’addar Daesh 55 daga cikin ‘yan ta’addar ISWAP.

Cikin wadanda aka kashe har da wasu manyan kwamandoji da dama ajihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar ma’aikatar tsaron kasar Nijar, rundunar hadin gwiwa ta Sector 3 da Sector 4 Multinational Joint ne suka shirya wani gagarumin farmaki na kwanaki 22 da aka yi wa lakabi da Operation HARBIN ZUMA, wanda aka fara a ranar 6 ga Mayu, 2023, kuma ya kare a ranar Lahadi 28 ga watan Mayu.

Wasu daga cikin manyan kwamandojin sun hada da Fiya Abouzeid, Qaïd Abou Oumama da Qaïd Malam Moustapha, da kuma wasu malaman addini da har yanzu ba a san sunayensu ba.

More from this stream

Recomended