Buhari ya ƙaddamar da ginin helkwatar hukumar Kwastam da aka kashe biliyan naira 19.6

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da sabon ginin helkwatar hukumar kwastam dake Abuja a ranar Talata.

An gina ginin ne a bayan ginin hukumar sadarwa ta ƙasa NCC dake gundumar Maitama a Abuja.

Da yake magana da yan jaridu a ranar Litinin, Bashir Adeniyi mataimakin shugaban kwastam na kasa ya faɗa cewa an kashe naira biliyan 19.6 wajen ginin ofishin.

More from this stream

Recomended