Babbar kotun jihar Katsina ta kori sababbin shugabannin kwamitin riko na jam’iyyar PDP dake jihar da aka naɗa.
Idan za a iya tunawa shugabancin jam’iyyar PDP na kasa shi ne ya naɗa kwamitin riko da zai jagoranci jam’iyyar bayan da ya amince da rushe shugabancin jam’iyyar a ranar 23 ga watan Maris.
Tsohon shugaban riko na jam’iyyar ta PDP, Salisu Uli shi ne ya shigar da karar inda ya nemi ya kori sabbin kwamitin riko da uwar jam’iyyar ta kafa.
Babban alkalin jihar, Mai Shari’a M.D Abubakar da ya jagoranci zaman shari’ar ya bayar da umarnin gaggawa da ya hana wanda ake ƙara na farko, Dr Abdulrahman Usman da kuma dukkanin mambobin kwamitin riƙon da su dai na ayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyar har sai an kammala sauraron karar da aka shigar gaban babbar kotun jihar.