An sako Farfesa Onje Gye Wado tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa wanda aka yi garkuwa da shi ranar Alhamis da daddare bayan da aka biya naira miliyan 4 a matsayin kuɗin fansa.
An sace tsohon mataimakin gwamnan nan ne daga gidansa dake kauyen su na Rinza kusa da garin Wamba hedkwatar ƙaramar hukumar Wamba ta jihar.
Tun da farko masu garkuwar sun bukaci a biya su miliyan N70 amma iyalansa suka yi tayin biyan naira miliyan N2 daga baya suka kara zuwa miliyan N3.5 kafin a karkare a miliyan 4.