Kotu ta bawa PDP umarnin hana dakatar da Ortom

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ye samu hukunci kotu da ya hana jam’iyyar PDP korarsa daga jam’iyyar.

Mai shari’a, A I Itoyonyin na babbar kotun jihar Benue, shi ne ya bayar da umarnin a ranar Alhamis biyo bayan karar da aka shigar gabansa mai namba MHC/46/2023 a ranar Laraba.

A karar an saka sunan hukumar zabe ta INEC da kuma jam’iyar PDP a matsayin waɗanda ake ƙara na farko da na biyu.

A hukuncin da ta yanke kotun ta bayar da umarnin wucin gadi da ya hana PDP “Kora, dakatarwa ko kuma aiwatar da duk wani matakin ladabtarwa akan Ortom.” har ya zuwa lokacin da za ta saurari karar.

More from this stream

Recomended