An kai hari kan magoya bayan Peter Obi a Lagos

Mutane da dame ne suka jikkata a harin da wasu yan bangar siyasa suka kai kan magoya bayan,Peter Obi dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Labour Party a jihar Lagos.

A ranar Asabar ne dai Obi ya gudanar da gangamin yakin neman zaben sa a filin wasa Teslim Balogun dake birnin na Ikko.

Magoya bayan Obi da dama ne suka fuskanci hare-haren lokacin da suke kan hanyar halartar taron.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Lagos, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da kai hare-haren kuma ya ce tuni sashen rundunar dake binciken manyan laifuka ya fara gudanar da bincike kan harin

More from this stream

Recomended