Rundunar yan sandan jihar Rivers,ta kama wani matashi dan shekara 17 da ake zargin da yiwa wasu mata 10 ciki.
Wanda ake zargin mai suna,Noble Uzuchi an kama shi da abokin ta’asarsa, Chigozie Ogbonna dan shekara 29.
A cewar hukumomi mutanen biyu da ake zargi da kuma wasu mata biyu Favour Bright da Peace Alikoi ana zargin su da samar da masana’antar da ake safarar jarirai.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Rivers, Grace Iringe Koko ta ce an samu nasarar kama mutanen ne bayan wasu bayanai da aka kwarmata musu.