
Rundunar yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wani matashi da ake zargi da kashe kishiyar mahaifiyarsa.
Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Matashin da ake zargi mai suna Gaddafi Sagir yayi amfani da sukun direba ya aikata kisan kan.
Kiyawa ya ce an kama yaron ne a wani kango lokacin da yake kokarin tsallake wa ya bar Kano.