NDLEA ta kama motoci biyu makare da tabar wiwi a Lagos

Hukumar NDLEA dake hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta samu nasarar kama wasu motoci biyu kirar siyana makare da ganyen tabar wiwi.

Kakakin hukumar Femi Babafemi shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

Babafemi ya ce jami’an hukumar sun kama Monday Michael wanda rikakken mai harkar miyagun kwayoyi ne a yankin Mushin-Isolo.

Michael na dauke da tabar wiwin mai nauyin kilogram 365. 7 a cikin motocin biyu masu namba FST 189 FD da FST 273 GF.

More from this stream

Recomended