Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya ziyarci Iyiola Omisore dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam’iyar SDP a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar.
Ganawar tasu na zuwa ne, kasa da sa’o’i 24 bayan da hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar da cewa zaben gwamnan jihar bai kammala ba.
Jam’iyar PDP ta koka kan cewa an yi mata ba dai-dai ba inda ta nemi da a bayyana dan takararta,Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben tunda shine wanda ya samu ƙuri’u mafi rinjaye.
A cikin yan tawagar shugaban majalisar dattawan a zuwa gidan jagoran jam’iyar ta SDP akwai Sanata Abiodun Olujimi daga jihar Ekiti da kuma Doyin Okupe daraktan yada labaran yakin neman zaben Saraki.
Ganawar na da nasaba da shirye-shiryen yadda za a hada karfi da karfe wajen kayar da jam’iyar PDP a zaben gwamnan jihar da za a sake yi a wasu mazabu ranar Alhamis.
Omisore ya amince yin aiki tare da Adeleke domin cigaban jihar.