
Biyo bayan harin da aka kai kan shingen binciken ababen hawa a kusa da Dutsen Zuma wani jarimin soja ya samu nasarar kashe yan bindigar biyu kafin shima ya mutu.
A ranar Alhamis ne da misalin karfe 08:00 na dare yan bindiga suka kai hari kan shingen binciken rundunar sojan Najeriya Bataliya ta 102 inda suka gamu da turjiya mai karfi daga sojojin.
A cewar wata majiya dake kusa da wurin bayan da yan bindigar suka gaza samun nasara sun sulale sun saje cikin al-ummar garin Gauraka dake kusa da wurin a bin da ya haifar da rudani.
Jami’in sojan shi ne yake aikin sanya idanu a shingen lokacin da lamarin ya faru inda ba kuma tare da bata lokaci ba ya fara mayar da wuta a yayin harin.
Lamarin dai ya jawo cinkoson ababen hawa a babbar hanyar da ta hada Abuja da Kaduna.