Yan bindiga sun sako yan kasuwar wayar Zamfara

Yan bindiga sun sako yan kasuwar wayar salula dake Gusau da suka yi garkuwa da su biyo bayan biyansu kudin fansa da aka yi.

Makonni biyu kenan da kama yan kasuwar lokacin da suke hanyarsu ta dawowa Gusau daga Sokoto inda suka je daurin auren abokinsu.

Dukkanin mutanen da aka sako na sana’a ne a kasuwar Bebeji Communication dake Gusau.

Wasu majiyoyi biyu dake kasuwar sun tabbatar da sako mutanen da misalin karfe 04:37 na yammacin ranar Alhamis.

“Mun biya sama da miliyan 10 kafin a sake su yau. Sun ce ɗaya daga cikin su ya mutu kwanaki biyar da suka mutu amma ba su fada mana ko waye ba,”ya ce.

More from this stream

Recomended