Hatsarin mota ya lakume rayukan mutane 18

A kalla mutane 18 ne suka mutu a wani hatsari da ya faru da tsakar safiyar ranar Lahadi a jihar Niger.

Lamarin ya faru ne a wajajen garin Gidan Kwano dake kan hanyar Minna- Bidda a ƙaramar hukumar Bosso ta jihar.

Dukkanin fasinjojin motar da aka ce ta taso ne daga Lagos sun kone kurmus.

Shedun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 05:00 na asuba.

Motar ta ci karo ne da wata babbar mota da take tsaye a titi.

More from this stream

Recomended