Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan mako na 29 a gasar La Liga da za su kece raini ranar Lahadi.
To sai dai kuma labari mara dadin ji ga Real Madrid shine Karim Benzema ba zai buga wasan na hamayya na El Clasico ba.
Dan wasan tawagar Faransa bai yi atisaye tare da abokan taka ledarsa ba, hakan na nufin ba zai samu damar yin gumurzu a Santiago Bernabeu ba.
Tun a wasan da Real ta yi da Mallorca, sai canja Benzema aka yi daf da za a tashi daga fafatawar, an kuma sa ran zai murmure tun farko kafin gumurzu da Barcelona.
Benzema ba zai samu damar fuskantar Barcelona wadda itace ta hudu a jerin kungiyoyin idan ya hadu da su sai ya ci kwallo mai 11 a raga, ya kuma bayar da 10 aka ci Barcelona a karawar da ya yi da ita.
Benzema shine kan gaba a cin kwallaye a gasar La Liga ta bana mai 22 kawo yanzu, sai Enes Unal na Getafe da Vinicius Junior na Real Madrid da kowanne keda 14 a raga.
Cikin ‘yan wasan dake cin kwallaye da Real Madrid ta bayyana da za su karbi bakuncin Barcelona sun hada da Hazard da Asensio da Jovic da Bale da Vini Jr. da Rodrygo da kuma Mariano.
A wasan farko da suka kara a babbar gasar tamaula ta Ingila a Camp Nou, Real Madrid ce ta yi nasara da ci 2-1.
Real Madrid tana mataki na daya da maki 66 a kan teburin La Liga na kakar nan, Barcelona kuwa mai kwantan wasa daya mai maki 51 tana ta uku a teburin.